Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Ceto Wani Yaro Daga Hannun Masu Fataucin Mutane


‘Yan Sanda sun ceto wani yaro Obinna Ozuoba, mai shekaru hudu da haihuwa daga hannu wasu masu fataucin mutane a jihar Abia.

Wani matashi Rowland Egbe, mai shekaru talatin da wata mata Chioma Ohajinmmadu, mai shekaru hamsin da haihuwa, su ake zargin akan yaro.

Shi dai yaron Rowland, ya yaudare shi ne da biskit, kafi ya samu jan ra’ayinsa, amma tuni aka mika shi ga iyayansa Mr. da Mrs. Uzoma Ozuoba.

Kwamishinan ‘yan Sandan jihar ta Abia, Leye Oyebade, ya ce an cafke Rowland, ne a Obehie, dake karamar hukumar Ukwa ta yamma, wanda daga bisani ya jagoranci ‘yan Sanda, zuwa gida mai lambar 16, dake layin Uchelekwa, a garin Aba, inda aka cafke Chioma.

Rowland, ya fadawa ‘yan Sanda cewa a can baya ya sayardawa Chioma, wata yarinya ta hannun wani dillali, akan kudi Naira dubu dari da hamsin inda aka bashi dubu hamsin.Amma ita Chioma, na miji take bukata domin acewarta ‘ya’yanta matane, a cewar Rowland, ya san yaron da iyayensa shi yasa yaron ya aminta dashi.

Kwamishinan ya ce rundunar ta sha alwashin ganin baya masu sana’ar fataucin mutane a jihar,yanzu haka dai rundunar ‘yan Sandan jihar na neman dillilin ruwa a jallo.

XS
SM
MD
LG