Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bincike Ya Bayyanar Da Jikin Dan'Adam Zai Iya Cajin Wayar Hannu!


Sinadarin Samar Da Wuta Ga Wayoyin Hannu
Sinadarin Samar Da Wuta Ga Wayoyin Hannu

Nan da shekaru kadan masu zuwa, za’a fara cajin wayoyin hannu da yatsun mutane. Taron masana bincike kimiyyar fasaha na jami’ar jihar Michigan, sun gano wata hanya da mutane zasu dinga amfani da tafin hannun su, wajen samar da wuta ga wayoyin hannu.

Jaridar “Nano Energy” ta ruwaito cewar, masanan sun kirkiri wani sinadari, da zai dinga amfani da motsin jikin mutun, a duk lokacin da mutun yayi motsi, wannan dan karamin mashin din, zai dinga jawo wuta daga cikin jikin mutun.

Haka zai bama wayar hannun caji cikin sauki, babu bukatar mutun sai ya saka wayar shi a caji na tsawon lokaci. Shi dai mashin din da suka kirkira kuma suka kirashi da suna “Nanogenerator” a turance, za’a iya amfani da shi a wayoyin zamani na hannu, da abun rubutu na kwamfuta “Keyboard” duk batare da sunyi amfani da batiri ba.

Shugaban binciken Farfesa Nelson Sepulveda, ya bayyanar da cewar, nan bada jimawa ba, har yaga mutane na amfani da wayoyin su a kowane hali, batare da bukatar ajiye wayoyin don caji ba. Haka wannan mashin din bashi da nauyi, wanda mutun zai iya sarrafashi wajen ajiya, kana bashi da tsada.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG