Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ban Yarda Dana Ya Rasu Ba - Inji Mahaifiyar Matashi Dan NYSC Da Ya Rasu A Jihar Zamfara


Mahaifiyar matashin nan mai aikin yiwa kasa hidima wanda ya rasa ransa a jihar Zamfara, ta bayyana bakin cinta, inda a kalamanta ta bayyana cewa da ma ita ta rasu a maimakon dan nata.

Matashin me suna Monday, wanda ya yi karatun Injiniya a bangaren albarkatun man fetur daga jami’ar Uyo dake jihar Akwa Ibom, ya rasu ne a yayinda suke karbar horaswa a karkashin rukunin B, na masu ayyukan yiwa kasa hidima a jihar Zamfara.

Biyo bayan bakin cikin rasuwar dan tahalikin, sashen koyon ayyukan injiniya na jami’ar da ya kammala karatu ta umurci dakatar da karatu na wasu ‘yan lokuta domin juyayin rasuwarsa.

Mai ba gwamnan jihar Akwa Ibom shawara kan harkokin ilimi da makamantansu Miss Otobang, tare da wasu dalibai sun kai ziyara gidan mamacin a wani gari da ake kira Etinan, dake jihar ta Akwa Ibom.

Mujallar Daily Post ta bayyana cewa mahaifiyar matashin ta yi ta kuka tana bayyana bakin cikin rasuwar dan nata, inda ta ke kuka tana fadawa wadanda suka ziyarceta cewar su koma su fadawa danta cewar tasan yana nan da rai, kuma tana dakon ganin dawowarsa bayan ya kammala aikin yiwa kasa hidima.

Ta ce kafin ya tafi ya yi mata alkawarin cewa zai dawo domin ya kula da ita bayan ya kammala aikin yiwa kasa hidima, alkawarin da ta ce take cike da zaton dan nata zai cika mata.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG