Ministan Matasa da Wasanni na Najeriya, Barista Solomon Dalung, ya ce Najeriya bata tsammaci kungiyar kwallon kafa ta Matan Najeriya Super Falcons zasu lashe kofin matan Afirka na shekara 2016, ba, wanda aka yi a kasar kamaru, shi yasa ba'a shirya biyansu alawus dinsu ba inda falcons suka doke masu masaukin baki matan kamaru daci daya da babu
Kungiyar kwallon kafa ta mata super falcons na cikin bakin ciki sakamakon rashin biyansu kudaden da suke bi bashi na samun nasarar da sukayi a gasar cin kofin mata na Afirka wanda hukumar NFF bata biya suba inda tun farko aka yi musu alkawarin za'a biya su.
Sanadiyar haka ne yasa 'yan wasan suka yi zaman dirishan a otel dake Abuja akan cewa sai an biyasu kafin su fita.
Ministan ya ziyarci 'yan wasan a masaukinsu na Agura otel Abuja, ya basu hakuri bisa wanan matsala da aka samu ta rashin biyansu akan lokaci, ya kuma ce suna tattaunawa da Jagororin hukumar NFF bisa wannan al'amari domin ganin an biya su nan bada jimawaba.
Sai dai hukumar ta NFF tace tun a kasar kamaru taba kowace 'yar wasa #500,000, sauran ragowarne aka samu matsala amma suna ta shirye shirye Don ganin an warware takaddamamar dake tsakani.
Wannan nasara da super falcons ta samu na lashe kofin matan Afirka shine karo na takwas da kungiyar ta samu