Sakonni Na Sun Danganci Muhimmancin Zaman Lafiya Da Amana -Inji Usainin Danko

Jabir wanda aka fi sani da fiddata Usainin Danko , ya ce kamar yadda masu iya Magana kan ce zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai, toh haka labarinsa ya ke, kasancewar ya zauna da wasu mawaka.

Jabir wanda ya ce yana isar da sakonnin da suka danganci muhimmancin amana da zaman lafiya a harkokin zamantakewa wanda yayi karanci a cikin al’umma.

Ya kara da cewa soyayya na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da zaman lafiya tsakanin kabilu da adinai, inda yake cewa shi a wajensa waka sana’a ce, domin aiki ne na dogaro da akai ga matasa.

A cewarsa a wannan lokaci da aiki yayi karanci wajibi ne matasa su kasance masu sana’o’in dogaro da kai , domin shi kam tuni ya samu ta sa sana’ar.

A fannin tsegumi kuwa ,fittaciyar jarumar nan ta Nollywood Tonto Dikeh, ta samu kyautar jarumar shekara ta peace award.

Tonto ta bayyana jin dadinta ne ta shafin sadarwa na Instagram inda take godewa Allah da masoyanta.

Your browser doesn’t support HTML5

Sakonni Na Sun Danganci Muhimmancin Zaman Lafiya Da Amana -Inji Usainin Danko