Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Jefa 'Yar Mijinta Cikin Rijiya Domin Kishi


Rundunar ‘yan Sandan jihar Kano, ta damke wasu matan aure ukku, da ake zargin da hannu a wani wunkuri na neman kashe wata ‘yarinya.

Kakakin rundunar DSP, Magaji Majiya, wanda ya tabbatar da labarin, yace an jefa yarinyar ne cikin wata tsohuwar rijiya, a kauyen Gayawa, dake karamar hukumar Ungoggo, a jihar ta Kano.

Kamar yadda Kamfanin dillancin labaran Najeriya, ta ruwaito tace yarinyar ta kwashe kwanaki biyu a cikin rijiyar da matar mahaifinta ta jefa ta cikin hukuncin Allah masu aikin kwana kwana sun fito da ita da rai.

Kakakin ‘yan Sandan yace kwamishinan ‘yan Sandan jihar Rabiu Yusuf, ya bada umarnin cewa a maida batun zuwa ofishin CID domin gudanar da bincike kamar yada yakamata, yana mai cewa duk wanda aka samu da hannu tabbaci hakika zai gurfana a gaban shara’a.

XS
SM
MD
LG