Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tayi Amfani Da Zarto Wajen Azabtar Da Marainiya


Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta cafke matan da ake zargi da asabtar da wata yarinya mai yi mata aikatau mai suna Esther.

Ita dai wannan mata Mfoniso Udodoikpom, ta asabtar da wanna yarinya ne inda tayi amfani da zarto, a dalilin cewa yarinyar ta fasa kwanon roba kuma ta kona girki.

Bincike na nuni da cewa ita dai wannan marainiya ‘yar shekaru goma sha ukku, matar ta dauko ta ne daga garinsu dake can jihar Akwa Ibom, ta kaita Legas, bayan rasuwar iyayenta, domin yimata aikatau a gida.

Kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Legas,Dolapo Badmus, da yake tabbatar da lamarin ya ce makwabci ne ya kawo rahoton ga hukumar ‘yan Sanda, ganin irin azabar da ake ganawa ita wannan marainiya.

Gwamnatin jihar Legas, ta ajiye marainiyar a wani matsugunni, inda ita kuwa Madam Mfoniso Udodoikpom, zata gurfana a gaban kotu domin amsa laifinta.

XS
SM
MD
LG