An tabbatar da Kate McWilliams, a matsayin matukiyar jirgin sama da tafi karancin shekaru a fadin duniya. Yanzu haka ta zamo shahararriyar matukiya a matakin “Captain” mafi karantar shekaru a tarihin tukin jirgin sama.
Kate, tana da shekaru ashirin da shida 26, a cewar kamfanin da takema aiki “Easyjet” Kate itace mace mafi karantar shekaru da take tuka jirgin kasuwanci a fadin duniya, wanda yanzu takai matakin Kaftin.
Zuwa yanzu dai ta ziyarci kimanin tashoshin jiragen sama fiye da dari a fadin duniya, sai suka kara da cewar duk inda ta tuka mutane suka isa waje, sai an yabamata da yadda take gudanar da aikin ta na tuki cikin hankali da tsanaki.
Ta samu horaswa a makarantar koyon tukin jirage, tun tana ‘yar shekaru goma sha uku 13. Yanzu haka ta samu nasarar cin jarabawar zama kaftin, a bangaren tukin jirgin sama. Ta bayyanar da cewar “gaskiya shekaru na ba wasu abun dubawa bane, da yadda nake gudanar da aiki na, na samu horaswa irin yadda ake bama kowa, kuma nayi kokari wajen cin jarabawar da ake ba kowa.”
Hakan ya bani damar zama abun da nake yanzu batare da la’akari da karanci shekaru na ba. Sai ta kara da cewar sau da yawa mutane kan tambayeni shekarun na. Yanzu haka dai tana sarrafa babban jirgin sama na "Airbus A319 da A320" don daukar fasinjoji zuwa ko ina a fadin duniya.
Ta kara da cewar, yanayin aikin ta, yana da dadi don kuwa takanyi fiye da wata daya kamin ta sake zuwa kasar da taje a cikin wata daya, hakan yana bata damar ziyarta wurare daban-daban a fadin duniya.
A cewar shugaban kungiyar mata matuka jirgin sama a kasar Birtaniya Julie Westhorp, Allah yasa dai Kate, tazama wadda zata kara bama mata sha'awar aikin tukin jirgin sama.