A shirin mu na wasu muhimman mata da suka taka rawa a cikin al’ummarsu a yau mun sami bakuncin matashiya Khadija Mohammad Audi, mai karatu a matakin karshe a sashen koyan aikin jarida . Ta ce ta samu damar shiga shirin Social entrepreneurship a kasar Amurka , inda su hudu daga nan gida Nijeriya suka sami wannan dama .
Khadija yar asalin jihar Katsina dake karatun digirinta a jam’iar Bayero ta Kano,ta ce ta samu labarin shirinne sanadiyar wani dalibi da suke karatu tare, ta ce an koya musu sana’oin dogaro da kai bayan sun bada jaddawlinsu na ayyukan dogaro da kai, tare da wayar musu da kai na yadda zasu tallafawa 'yan uwansu matasa idan sun dawo gida Nijeriya.
Ta ce sun je jihohi biyar a kasar Amurka yayin da suka yi wasu awowi a jihohi uku.
Khadija ta ce jadawalinta ya maida hankali kan matasa masu shaye-shaye a kan tituna tare da almajirai da suke yawo suna bara batare da sun amfana da rayuwarsu wajen zama masu dogaro da kai.
Ku biyo mu domin jin cikakkiyar hirar wakiliyar Dandalinvoa da Khadija Audi.
Your browser doesn’t support HTML5