Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta Nigeria (NFF) ta umurci sabon Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Gernot Rohr da ya fitar da Sunayen ‘yanwasa guda 23 wadanda zasu fafata da kasar Zambia a wasan nema shiga gurbin cin kofin duniya na shekara 2018.
‘Yan wasan Nigeria dai zasu fafata ne da Chipolopolo na Zambia ranar 9/10/2016 acan kasar ta Zambia
Sabon Mai horar da ‘yan wasan na Super Eagles, Gernot Rohr dan kasar Jamus, ya fara samun nasara a wasansa na farko da ya jagoranci Super Eagles, da ta buga da kasar Tanzania, aka kuma tashi daya da nema.
Wasan dai na neman gurbi ne a gasar neman shiga cin kofin kasashen Afirka wanda za'ayi a 2017 a kasar Gabon .
Duk da nasarar da Najeriya,ta yi bai bata damar hayewa ba a rukunin, NFF ta ce tana bukatar ya fitar da Sunayen nan da sati mai zuwa.