Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Gaske Wayoyin Hannu Da Makamantan Su na Yada Cututtuka?


Wayar Hannu
Wayar Hannu

Domin gujema cututtuka da ake dauka tsakanin mutane, wasu taron masana sun bayyanar da wasu abubuwa guda shida, da suka tabbatar da cewar suke yada cututtuka a tsakanin jama’a. Batare da mutane sun bada hankalin su wajen ba.

Magananin wadannan cututtukan guda uku ne, mutun ya kokarta yin allurar riga kafi, a wannan yanayin, haka a guji zama da mutane dake da mura ko wata cuta da wani kan iya dauka, sai a hanzarta don tsaftace muhalli da wanke ko gyara wajen bayan tashin mara lafiya.

Wayoyin hannu na daya daga cikin hanyoyin da ake daukar cuta cikin sauri da sauki, yadda mutane ke rike waya a hannu bayan cuttuka sun gama zagaye wayar. Haka da yadda mutane ke shiga wajen jama’a batare da saka wani kariya ba, koda kuwa wajen bude kofa ne, don wani yana dauke da wata cuta kuma ya sakata a jikin hannu kofa.

Hakama mutane suyi hattara da yadda suke amfani da irin kayan da akanyi aron su, kamar kaset, rumot control, da dai makamantan su. Da kiyaye wadannan abubuwa ne kawai mutun zai iya gujema cututtuka dake yaduwa a tsakanin mutane, musamman a wannan yanayin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG