Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Wasu Matasa Masu Lalata Wutar Lantarki


Jami’an rundunar tsaron kasa ta Najeriya, ta cafke wasu matasa ukku, da ake zargi da laifin lalatawa da satar wayoyin wutan lantarki, a Awka dake jihar Anambra.

Wadannan matasa dai sune Nnamdi Nweke, mai koyon aikin kiran zamani watau walda, Chibuzor Mouta, mai sana’ar sayarda da lemu, da kuma Ikechukwu Okafor, mai sayarda gyada.

Duk wadannan matasa da aka kama suna bannata wayoyin wutan lantarkin ‘yan asalin garin na Awka ne.

Da yake ganawa da manema, labarai kwamandan rundunar tsaron na jihar Anambra Mr. Godwin Omoregie, ya bayyana cewa alokacin da jami’an rundunar ke sintiri ne suka yi kicibus, da wadannan matasa masu satar wayan lantarki.

XS
SM
MD
LG