Rundunar ‘yan Sandan jihar Abia ta damke wani Boka, bayan ta ta same shi da wasu bangarorin mutane da kasusuwa.
Kwamishinan ‘yan Sandan jihar Mr. Leye Oyebade, ne ya shedawa manema labarai a garin Umuahia, cewa mutumin da aka damke, ya kasa baiwa hukumomin wani dalili mai gamsarwa a lokacin da akayi mashi tambayoyi.
Yana mai cewa kwarangwal din kai da wasu kasusuwan da aka samu an zargin na irin mutanen da ake kashewa ne.
Wanda ake zargi ya musanta zargin yana mai cewa yayi gadon sune a wurin wani kawun sa wanda shima boka ne kafin rasuwarsa.
Yace mutanan su ne suka kai karansa wajen ‘yan Sanda domin yana amfani da kasusuwan wajen yin siddabaru.
Ya kara da cewa duk wanda ya taba sai mazakutan say a bace idan har kasusuwan na tare dashi.
Shi dai wannan Boka wanda kuma magini ne ya ce ‘yan Sandan sun yi nasarar damke shine saboda asirin da yake amfani dashi yayi balaguro, da cewa kama shi da akayi ba daidai bane saboda haka ya bukaci da a sake shi.