WASHINGTON D.C —
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya umurci kwamishinan ‘yan sandan kasar Augustine Chihuri cewar ya kame da kuma tsare dukkan ‘yan wasan kasar da suka halarci gasar wasannin motsa jiki da aka kammala kwanan nan a kasar Brazil.
Wannan umrni na shugaban kasar ya kasance ne a sakamakon rashin tabuka abin kirki da ‘yan wasan suka yi a lokacin da ake gudanar da wasannin.
Kasar na cikin kasashen da suka koma gida hannu rabbana ba tare da lashe kyauta ko guda ba, duk da yake kasar ta sami wakilcin ‘yan wasa talatin da daya, 31 da suka fafata a wasanin daban daban.
Shugaba Robert Mugabe ya zargi ‘yan wasan da rashin kishin kasa tare da bannata dukiyar kasa ba tare da kawo komi gida ba.