Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nesa Tazo Kusa! Manhajar "Whatsapp" A Kan Kwamfuta Cikin Sauki!


Whatsapp
Whatsapp

Nesa tazo kusa! Mutane zasu iya amfani da na’urar kwamfutar su, ko kuma na’urar tafi da gidan ka, don amfani da hanyar sadarwa ta “Whatsapp” wannan wata damace da mutane zasu dinga amfani da datar su, don gujema karar da ita wajen magana da mutane cikin sauri.

Yanzu dai haka mutun idan suna bukatar hada wazob din su, da kwanfuta, abu kawai da mutun zai bukata shine, ya shiga shafin www.whatsapp.com sai ya bude wayar shi, yaje inda akace sashen wazob “Whatsapp Web” daga nan sai ya haska wayar shi, zuwa ga shafin da ya bude a kan kwamfutar shi, wani bakin layi zai fito, wanda kyamarar wayar shi zata dauka hoto.

Mutun koda kuwa wace irin waya yake amfani da ita, zai iya saka wannan manhajar a kan kwamfutar shi, a kowane lokaci yaso yin hakan. Daga nan mutun zai ga duk wasu abubuwa da ya keyi a wayar shi sun koma kan kwamfutar shi. Da wannan damar babu abun da mutun ba zai iya yi ba wanda ya saba yi da wayar shi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG