Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Iya Magana Sun Ce Wanda Baiji Bari Ba...


‘Yan Najeriya 241 wadanda da yardar kawunansu suka bukaci a dawo dasu gida daga kasar Libiya sun sauka a tashar jirgin sama dake jihar Legas da misalign karfe goma sha biyu na rana.

Da yake hira da manema labarai shugaba mai kula da sashen tafiye tafiye zuwa kasashen waje ya bayyana cewa matafiyan su dari biyu da arba’in da daya sun sami kawunansu cikin halin kakanikayi a kasar ta Libiya, kuma sun bukaci a dawo dasu gida ne domin kansu.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikinsu sun sami matsala ne da hukumar shigi da fici ta kasar Libiya, wasu kuma sun yi yunkurin ketarawa turai ne amma hakarsu bata cima ruwa ba.

Matafiyan sun hada da mata da maza da kuma kananan yara, kuma su da kansu suka bukaci a dawo da su gida Najeriya.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG