Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar JAMB Ta Bada Albishir Ga Jami'o'i Da Dalibai


Hukumar jarawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta tabbatarwa da jami’o’I da sauran makarantun gaba da sakandire cewar bazata yi katsalanda a jerin sunayen da daliban da ta mikawa makarantun domin basu guraben karatu na shekarar 2016 ba.

Sanarwar ta fito ne a yayin da hukumar ke cigaba da gudanar da taron shawarwari akan bada guraben karatu a jami’o’I da sauran makarantun gaba da sakandire na wannan shekarar a jami’ar Bayero dake Kano, inda shugaban hukumar Farfesa Is-haq Oloyede ya aikawa manema labarai a babban birnin tarayya da sanarwar bayanan ta email.

Shugaban ya bayyana cewa ya dukufa wajan tabbatar da ganin cewar an kammala ayyuka da kuma fitar da jerin sunayen daliban da suka sami nasarar samun guraben karatun kafin kokuma a ranar karshe da aka tsayar domin fitar da jerin sunyen wato 30, ga watan Nuwambar wannan shekara da muke ciki.

Ya kuma yi gargadin cewa babu sunan dalibi ko dalibar da zai fito daga wata kafa daban baya ga sunayen da mayan makarantun suka tantance kuma suka wallafa.

Farfesa Oloyede ya kara da cewa kamar yadda aka saba, za’a fitar da jerin sunayen daliban ba tare da wata matsala ba, ya ce banbacin bada guraben karatun na bana ya bambanta da na shekarun da suka gabata ne kawai ta yadda dalibai baza su sake rubuta wata jarabawa ta UTME da jami’o’i k aba dalibai ba. Amma dukkan hanyoyin tantancewar na nan kamar yadda suke a da.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG