Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Dalibai 8 A Jihar Zamfara


Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafinsa na Twitter yayi Allah wadai da tashin hankali da kisan dalibai a makarantar kimiyya da fasaha ta Abdu Gusau Politechnic dake karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, sanadiyyar rikici akan zargin batanci da wani dalibi guda yayi ga Annabi Muhammadu (SAW).

Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin wanda ya hassada rikicin dalibi ne a makarantar, kuma ya doki wanda ake zargi da yin batancin kana ya cinnawa gidan da yake ciki wuta, lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane takwas dake cikin gidan.

Shugaba Buhari ya bayyana kaduwa da nuna rashin jin dadin kasancewar lamarin a shafinsa na twitter inda y ace “na sami labarin masifar da zanga zangar da dalibai suka yi a jihar Zamfara da abinda ta haifar, wannan jahilci ne kuma ba irin abin da zamu amince da shi bane. Ina mai tabbatar da cewa doka zata dauki mataki akan abinda ya faru”.

Lamarin ya faru ne a dai-dai ranar da sakataren harkokin Amurka John Kerry ya kai ziyara a kasar a karkashin sabon shirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yiwa lakabi da cewa “a karkashin kulawata zamu yi aiki tare domin tabbatar da kauce wa amfani da addini, ko kabilanci da sauran abubuwa makamantan su wajan duk wani tada zaune tsaye”.

Mujallar Vanguard ta wallafa cewa a lokacin da ta fitar da rahoton jami’an ‘yan sanda masu gudanar da bincike basu bada sanarwar nasarar samun zakulo wadanda ake zargi da haddasa tashin hankalin ba, wadanda ake zargin akasarinsu dalibai ne.

Kawo yanzu dai hukumomin makarantar sun dakatar da gudanar da dukkan ayyukan makarantar har sai abinda hali ya yi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG