A kalla mutum guda ya mutu sannan wasu 25 sun samu raunuka jiya Laraba, a wani harin da aka kai a Jami'ar Amurka da ke Kabul, babban birnin Afghanistan.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Lafita ta Afghanistan, Wahed Majroh, ya gaya ma Muryar Amurka cewa cikin wadanda su ka ji raunuka har da wani furfesa da wasu dalibai mata biyu. Bai yi karin bayani kan mutanen da su ka mutu din ba.
An yi imanin cewa dalibai da ma'aikata da dama na makale cikin jami'ar, bayan harin da aka fara shi da tarwatsa bama-bamai.
An fara kai harin ne da misalin karfe 6:30 na yamma agogon wurin, wanda ya janyo musayar wuta yayin da jami'an tsaro su ka mai da martani. Har yanzu ba a san adadin wadanda su ka kai harin ba. Jami'ai sun bayyana harin da "mai daure kai."
Wani mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Cikin Gidan Afghanistan, Sediq Seddiqi, ya gaya ma Muryar Amurka cewa jami'an tsaro na kokarin ceto wadanda ke cikin jimi'ar. Sojojin Afghanistan na musamman na zagaye da jami'ar.
Wani dalibi da ke makale cikin jami'ar ya gaya ma kafar labarai ta Reuters ta waya cewa da shi da wasu mutane na makale cikin wani aji. Ya ce su na jin karar wutar bindiga daga waje.
Shi kuwa wani dalibi da ya tsere, Massoud Hossaini, ya gaya ma Associated Press cewa, shi ma sai da ya makale tare da wasu dalibai a wani aji, inda su ka tare kofar da kujeru da tebura. Ya ce daga bisani sun lallaba sun sulale ta wata boyayyiyar kofar jami'ar da ke arewa.