Aicha MACKY, yar asalin jihar Zinder ce, a kasar NIGER. An haife ta a cikin garin Zinder, inda tayi makarantan firamare a makarantar Zengou fille da kuma karatun sakandire a CEG II. Tayi karatu a lycée AMADOU KOURAN DAGA inda tayi nasarar cin jarabawar shiga jami'ar Abdou Moumouni ta Niamey a Niger a 2004. Ta samou degree a fannin ilim sanin hallayan dan’adam “Sociology” a shekara 2010.
Bayan haka ta yi karatu a makarantar ‘yan jarida wadda ake kira IFTIC a nan cikin Niamey inda ta futo da degree na fannin jarida. Daga nan sai tasamu talafin “Region Rhones alpes” wato kassar farensa inda ta je Sénégal ta yi karatun tsara film fannin documentary a jamiar Gaston Berger ta Saint-Louis. Ta futo hal ila yau da degree.
Aicha, tayi zaman aiki da masu bincike da hazaka inda ta lura cewa mafi yawan cin littatafan, da ake rubutawa da yaren farancenci basa samun karbuwa, ganin cewa mafi yawan al'umar Niger, basu yi karatoun boko ba. Sabo da haka ne ta bada kaimi wajen shirya finafinai da yaran kassar su musamman ma Hausawa.
Dan ganin ta janyo hankalin al'umma game da matsaloli da dama da su ke damun al'uma kamar rashin tattaunawa tsakanin iyaye mata da diyan su mata, da duk abin da ya shafi ‘yancin mata da yara da kuma girka zaman lafiya a kassar Niger.