Fatima Sharif Mahmoud matashiya da ta hasasa kungiyar tallafawa marayu mata da kananan yara , a makon da ya gabata sun ziyarci Nassarawa orphanage home , da ke daff da asibitin nasarawa a kanon Nigeria ,ta ce tun tana karama ta ke da burin taimakawa masu kananan karfi, wanda hakan ne ma ya sa ta fara bada tallafi tare da hadin guiwar yan uwa da ke cikin kungiyar ta su .
Ta ce kungiyar da ta kewa shugabanci mai suna “Initiative For The Less Privilege Women And Children” ta kafa kungiyar ne da niyyar taimakawa mata da yara mabukata.
Abinda take jin dadin yin a kowane lokaci shine taimakawa mutane masamman marayu da mabukata, tana mai cewa duk kayayyakin da suka kaiwa gidan marayun daga aljuhun ta da na ‘ya’yan kungiyar ya fito.
Hajiya Biliksu Waziri babban sakatariyar ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Kano, ta ce lallai mutane na kokartawa wajen kawo tallafi ga wannan gida, inda ta ke cewa gidan marayun dake asibitin nassarawa gidan yan gata ake ce musu ba gidan marayu ba saboda irin yadda gidan ke samun kulawa daga jama’a dama da hagu.