Amfani Da Wayoyi Masu Manhajar Android Na Bukatar Taka Tsan-Tsan!

Satar Bayanai ta Amfani da Malware

Malware, wata manhaja ce da aka kirkira don shiga wayoyin android na mutane da zummar satar musu bayanai. Kimanin mutane sama da milliyan goma 10M, ne suka zama cikin jerin mutanen da wannan sabuwar basirar ta shafa.

An kirkiri wannan manhajar ne don inganta wayoyi masu manhajar android, wanda daga bisani wasu bata gari, suka samu damar shiga shafin kamfanin don satar bayanan mutane a fadin duniya. A cewar kamfanin sukan samu kudi da suka kai kimanin milliyan dari uku $300,00 a aikin su na aika talla da wasu abubuwa, da suke samarwa ga masu wayar android.

Mafi akasarin wayoyin kirar kasashen China, India, da Philippian, ne wannan manhajar satar bayanan tafi shafa. Duk mutane da suke amfani da irin wadannan wayoyin, sai su kokarta wajen ganin cewar ba komai suke saukarwa a wayoyin suba, don tahaka ne akan samu damar shiga wayar su har ayi musu kutsen labarai dama abubuwan sirri na bankunan su.