Garin “Ashkelon” wani karamin gari ne a kasar “Israel” dake daular kasashen larabawa, garin na da tsohon tarihi a duniya. A karon farko an hako kasusuwan wani basamude, kashin dai ya banbanta da na yadda mutane suke na wannan zamanin.
Jim kadan bayan hako wannan kashin, masu binciken arzikin tarihin karkarshin kasa “Archeologists” a turance, sun bayyanar da wannan kashin da cewar ba kashin mutanen wannan zamanin bane, kashin yayi kama da na wasu mutane da sukayi zamani da annabawa. Akwai alamun gashin nan ya kwashe sama da shekaru dubu biyu 2000, a cikin kasa
A tarihin annabawa, an bayyanar da Samudawa a matsayin mutane da suke da girman jiki, fiye da na yadda mutane suke a wannan zamanin. Hakan yasa masu binciken suka tabbatar da cewar wannan kashin wani basamude ne a wancan zamanin.
Sun bayyanar da wannan a matsayin babban cigaba da zai bayyana ma mutanen wannan zamanin yadda samudawa suke na wancan zamanin. Yanzu haka dai suna kokarin daukar kasusuwan don bincika da gano yadda samudawan suke gudanar da rayuwar su a wancan lokacin.