WASHINGTON D.C —
Masu bincike na hukumar kare haduran kan hanya ta tarayyar Amurka, sun bukaci kamfanin nan mai kera motar lataroni mai suna Tesla Motors da ya gabatar ma su da cikakken bayani kan na'urar da ke tuka motar.
Wannan ya faru ne saboda mummunan hadarin nan da ya auku a farkon wannan shekarar lokacin da irin wannan na'urar ke aiki.
A wata wasikar da aka bayyana ma jama'a jiya Talata, Hukumar Kare Haduran Manyan Hanyoyi Ta Kasa ta bukaci a bata bayanan dukkannin haduran da ke da alaka da cikas din na'urar da ke tuka motar da aka makala ma motocin Tesla din, wadanda su ka auku tun bayan da aka fara aiki da na'urar bara.
Hukumar ta kuma bukaci a mata bayanin irin gyaregyaren da za a yi ma na'urar cikin watanni masu zauwa.