Duk wanda yasan tarihin Mikiya “Eagle” a turance, yasan wata irin dabbace mai karfi, kana tana farautar namun daji don cin abinci. Mafi akasarin wannan tsuntsun akan same shi a cikin kungurmin daji ne. A duk lokacin da namun daji suka fahimci cewar yana shawagi don neman abinci, to kuwa a wannan lokacin kawane dabba zai sha jinin jikin shi. Mikiya kan dauki dabba da nauyinta yakai kimanin nauyin buhun siminti.
A ranar litinin da ta gabata, hukumomin gandun dajin “Alice Springs Desert Park” a kasar Australia, sun fitar da wani rahoto da ya tabbatar da yunkurin wani mayunwacin mikiya, da yayi yunkurin sace wani yaro, a dai-dai lokacin da suka kai ziyarar ganin gari da shi da mahaifiyar shi.
Kimanin shekaru dari 100, da suka wuce an samu matsalolin mikiya da satar yara, a wannan shekarar ma sai ga hakan ya faru. Duk dai da cewar mikiyar tayi yunkuri amma batasamu nasara ba, domin kuwa yaron yana sanye da riga mai hula, da yasa mikiyar bata kama kan yaron da kyau ba.
Hakan yasa yaron ya tsira amma da rauni, yanzu haka dai yaron yana asibiti don jinya na rauni da ya samu a sanadiyar yunkurin mikiyar. Don mikiya kanyi amfani da kunba wajen daukar duk wani abu da take bukata.