Kamfanin jiragen sama na Emirates Air, shine kamfanin da ya lashe lambar jinjina na kamfanin jirage da yafi kowane jirgi nagarta da kyautatama abokan hurda, na shekarar 2016. An yabama kamfanin da lambar yabo ta “Skytrax World Airline Awards” Wannan iatce karramawa mafi girma da kamfanin jirgi na duk fadin duniya zaiso samu.
Kamfanin dai ya kwashe shekaru uku 3, kenan yana lashe wannan kyautar a jere a jere, an tabbatar da cewar kamfanin shine kamfanin jiragen sama da yafi kowanne mutunta abokan hurdar shi. Kamfanin Qatar Airways, shine kamfanin da yake zuwa na biyu 2, a kowace shekara, sai kamfanin Singapore, yazo na uku 3.
Kanfanin Turkish Airline, shi ne kamfanin da yazo na bakwai, kuma shine kamfanin yankin kasashen turai da ya zama na farko a cikin jerin. Kana kamfanin Lufthansa, shima ya shiga cikin jerin kamfanoni da suka samu lambar yabo. Haka a wajen bayyana wanda ma’aikatan su, su kafi tsafta, kamfanin Emirate Air, sune na farko.1.Emirates 2.Qatar Airways 3.Singapore Airlines 4.Cathay Pacific 5.ANAAll Nippon Airways 6. Etihad Airways 7.Turkish Airlines 8.EVAAir 9.Qantas Airways 10. Lufthansa.