Kamfanin Facebook ya nuna ra’ayinsa na game duniya ta yanar gizo, wannan na nufin cewa karuwar yawan jama’ar da zasu yi amfani da yanar gizo zata iya kasancewa su yi amfani da shafin sada zumunta na facebook, dan haka tallace tallacen da ake yi a shafin zasu kara budewa kamfanin hanyoyin samun kudaden shiga.
Ta dalin haka ne kamfanin ya kirkiro wata yar karamar na’ura da mai amfani da shafin zai makala a duk inda yake kuma zata samar masa da network na yanar a gizo a duk inda mutum yake a duniya domin ziyartar shafin.
Na’urar wadda kamfanin ya sawa suna OpenCellular bata da wani girma kuma za’a iya Makalata a jikin ice ko a kafa sanda a Makala ta akai kokuma jikin bango, kana a sa mata batiri ko wutar lamtarki sai kawai ta ba masu amfani da ita network mai karfin da zasu iya amfani dashi domin shiga shafin a kowane lokaci.