A wata sanarwa da kungiyar tsagerun Niger Delta, ta fitar wace ke kiran kanta da sunan Niger Delta, Avengers, kungiyar ta sha alwashin durkusar da tattalin arzikin Najeriya, kuma ga dukkan alamu suna samun nasara.
Domin jirin hare haren da ‘yan kungiyar ke kaiwa kan bututun mai ya rage yawan man da kasar ke fitarwa, Gail Anderson, shugaban kungiyar dake bincike fanin samar da mai ta Wood Mackenzie tace hare hare nana kai sune masamman domin kassara yawan man da ake fitarwa a rana.
Tace hare haren an shirya su da kyau da zammar haifar da mummunar asara kuma daga dukkan alamu suna samun galaba.
Yin kididdigar girmar asarar da Najeriya ke tafkawa a fanin fitar da danyan mai zuwa kasashen waje wani abu ne da ba za’a iya fada nan take ba.
Najeriya, ta kan fitar da kusan gangar danyan mai miliyan 2.2 a kowace rana kuma a ganin Anderson, hakan ya ragu zuwa gangar mai dubu 560, wato kashi 25, cikin 100.
Shugaban sashen gudanar da bincike na fannin mai na Ecobank, Dolapo Oni, yace man da Najeriya ke fitarwa ya koma kasa da miliyan daya a rana.
Tattalin arzikin Najeriya, dai ya ragu a watannin ukun karshe, kuma masu fashin baki sun ce Najeriya, ka iya fadawa cikin matsalar tabaarbarewar tattalin arziki nan bada jimawa ba.
Baya ga haka faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, shima ya shafi tattalin arzikin kasa, kuma Najeriya na bukatar kowane digon mai domin ciyar da kasar gaba.