Kamar yadda aka ji daga bakin wani babban jami'in majalisar kula da 'yan gudun hijira daga kasar Norway take cewa halin da farar hula ke ciki nada ban tausayi
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD a takaice, ta sami rahotannin cewa ana kashe farar hula sakamakon amfani da manyan makamai, wasu kuma baraguzan gine ginen gidajensu da suka fadi sun danne su.
"Haka nan akwai rahotannin cewa daruruwan iyalai ne aka ce kungiyar ISIS take amfani da su a zaman garkuwa" na hana akai musu hari, inji kakakin hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD William Spindler.
Ahalinda ake ciki kuma a Syria, jiragen yaki da ake kyautata zaton na kasar Rasha ne, sun yi luguden wuta kan birnin Idlib dake hanun 'yan tawaye, suka kashe akalla mutane 50 suka jikkata wasu masu yawa, sannan da wasu da ake jin gine-gine da suka rushe sun danne su.