Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Habasha Sun Tsare Wani Fitaccen Dan Hamayya Kan Zargin Ta'adanci


Firayim Ministan Habasha Hailemarian Desalegn
Firayim Ministan Habasha Hailemarian Desalegn

A Ethiopia, hukumomin kasar suna zargin wani fitaccen dan hamayya, Yonatan Tesfaye da laifin ta'addanci. Amma makamin da ake zargin yayi amfani da shi ba binidga ko bam bane, ko kuma dan wata kungiyar addini ta 'yan gani kasheni.

Yonatan wanda tsofon kakakin jam'iyyar da ake kira Blue ko Semayawi ana tsare da shi ne tun cikin watan Disemban bara, karkashin sashe na hudu na dokar yaki da ta'addanci da kasar Habasha ta kafa. Gwamnati tayi amfani da rubuce rubucen da yayi a dandalin Facebook a zaman shaida. Dan hamayyar ya soki lamirin gwamnati kan matakan da gwamnatin tayi amfani dasu wajen murkushe zanga zangar da wasu suka yi a yankin Oromo. Gwamnatin tana zarginsa da shirin zuga jama'a su yi ta'addanci. Lauyan sa ya musanta haka yana cewa tsarin mulkin kasar ta baiwa Yonatan 'yancin bayyana ra'ayinsa.

Kamar yadda kungiyar Amnesty mai rajin kare 'yancin Bil'Adama ta bayyana wannan matsala ba kasar Habasha kadai ake fuskantar irinta ba,inda tayi zargin dokoki da aka kafa domin yaki da ta'addanci gwanatoci suna kara amfani dasu wajen hana 'yan hamayyar siyasa, da 'yan jarida, da 'yan kungiyoyin farar hula yin magana.Banda Ethiopia inji Amnesty, wasu kasashen Afirka da suka kafa irin wadannan dokoki a baya bayan nan sun hada da Kamaru, da Kenya, da Najeriya da Uganda.

XS
SM
MD
LG