Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayyana Sunayen Wadanda Suka Sace Dukiyar Kasa Hakkin 'Yan Najeriya Ne - Abubakar Ali


Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammad Buhari

Bayan da shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya yiwa 'yan kasar jawabi yayinda yake bikin cika shekara daya kan mulki, cecekuce ya biyo bayan kasa bayyana wa 'yan kasar sunayen wadanda suka yi sama da fadi da dukiyar kasar

Tun farko shugaba Buhari yace kasar ta kwato dubban dubatan biliyoyin nera da daloli da kuma wasu dukiyoyi daga wasu jam'ai da gwamnatin ta gano cewa sun yi sama da fadi da dukiyoyin kasar.

Wasu 'yan kasar sun dage cewa lallai lokaci yayi da shugaba Muhammad Buhari ya kamata ya cika alkawuran da ya yi masu. Ya fada masu cewa zai shaida masu jerin sunayen mutanen da suka yi sama da fadi da dukiyoyin kasar.

To saidai shugaban ya bada dalilan da suka sa ba zai iya gabatar da sunayen mutanen ba a yanzu domin yin hakan ka iya sabawa wasu dokoki ko sharudda na shari'a. Ya fadawa manema labaru cewa maganar yanzu tana kotuna da dama kuma gabatar da sunayensu ka iya kawo sabani ko kuma zagon kasa ga kokarin yaki da cin hanci da rashawa.

A kan haka wani dan fafutikar yaki da cin hanci da rashawa Abubakar Ali yace lallai 'yan kasa nada hakkin a gaya masu wadanda suka yi sama da fadi da dukiyar kasarsu. Saidai yace idan a cikin yarjejeniyar da aka yi akwai wadanda a bayan fage an matsasu tare da tilasta masu suka maida kudaden gwamnati to a irin wannan, inji Abubakar Ali, akwai ayar tambaya. Idan a cikin yarjejeniyar an ce ba za'a bayyana sunayensu ba to ko shakka babu ba'a kyautatawa 'yan kasar da kasar ba. Abubakar Ali yace irin haka ka iya haifar da yawan jita-jita.

Malam Ali yace amma irin wadanda aka riga aka gurfanar dasu gaban shari'a to bai kamata a bayyana sunayensu ba domin shari'a ce kawai zata tabbatar cewa mutum barawo ne ko ba barawo ba.

Haka ma Dr. Junaidu Muhammad, tsohon dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya yace lallai da walakin goro a miya. Yace a ganinsa kamata ya yi a bayyana sunayen wadanda aka kwato kadarorin kasar daga hannunsu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG