Amurka Zata Taimaka Da Dala Miliyan Arba’in Domin ‘Yan Gudun Hijira

Samatha Power

Samatha Power Ta Kaiwa ‘Yan Gudun Hijira Ziyarar Gani Da Ido

A karon farko na ziyarar, jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin duniya Samatha Power, zuwa kasar Kamaru, ta tattauna da shugaba Paul Biya, akan yadda kasashen biyu zasu cimma nasara kan yaki da ‘yan Boko Haram, da matsalar sauyin yanayi.

Da take yiwa manema labarai jawabi Samatha Power, tace sun tattauna kan hanyoyin da kasashen biyu zasu bi na murkuse ‘yan kungiyar Boko Haram, sa’ilin na mun amince zamu yi iyaka cin bakin kokarin mu domin murkushe ‘yan Boko Haram, cikin lokaci kankani.

Samatha Power, ta zarce da ziyarar nata ne zuwa ofishin Ministan Dabbobi da albarkatun gandun daji, inda ta jagoranci kona hauren Giwa sama da tan 500, a birnin Yaounde.

Daga nan sai arewa mai nisa domin gani da ido yadda ‘yan gudun hijira dake Mini Wawo, a sansanin da Majalisar dinkin duniya ta gina masu tantuna, ida yawan su yake kimanin 50,000 inda kuma wasu ke warwatse a yankunan tafkin Chadi.

Jakadiyar tace zasu taimakawa kasashen Niger, Nigeria Chadi da Kamaru, Amurka zata taimaka da dala miliyan arba’in domin ‘yan gudun hijira.