Zanga-zangar ta ci karo da matakin mumunar murkushewa da jami'an tsaro suka dauka kuma kungiyar Amnesty International ta ce akalla mutum 13 sun mutu. Amma jami'an tsaro sun musanta yin amfani da muggan makamai.
An dai gurfanar da mutanen 10 a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda kuma suka shigar da karar ba su da laifi. Suna fuskantar hukuncin kisa idan har aka same su da laifi, in ji lauyan kare hakkin ‘dan Adam Inibehe Effiong.
Masu shigar da kara na kasa sun ce a cikin takardun kotu da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani, masu zanga-zangar sun yi nufin kawo cikas ga zaman lafiya a Najeriya ne kuma "sun hada baki tare wajen aikata laifi, da cin amanar kasa".
Masu gabatar da kara sun kuma gabatar da wasu tuhume-tuhume guda biyar a kan wadanda ake tuhuma a karkashin dokar hukunta manyan laifuka ta kasar, da suka hada da ingiza sojoji su yi juyin mulki, kona gine-ginen gwamnati da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar jama'a.
Lauyoyin masu zanga-zangar dai sun nemi a sake su bisa belin to sai dai gwamnatin kasar ta nuna adawa da hakan.
Kotun za ta yanke hukunci a ranar 11 ga watan Satumba lokacin da ake sa ran za a fara shari'ar tasu.
Kungiyar Amnesty dai ta bukaci gwamnati da ta saki dukkan mutanen da aka kama yayin zanga-zangar ba tare da wani sharadi ba.
Ta ce an yi shari’ar ne domin a ba da hujjar tsare masu zanga-zangar ba bisa ka’ida ba.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna