Zanga-zangar da aka safe kwanaki 10 ana gudanar da ita tayi sanadin kara hauhawar farashin kayan masarufi, karin kudin mota, da dai sauransu.
Siradjo Sani Mai Kaset, mazaunin kasar Nijar ya ce wannan zanga-zangar su mazauna Nijar ba su yi fatan da ma su yi ta ba, to yanzu ba zanga-zanga ce ma matsalar ba, a’a irin asarar da aka jawowa ‘yan kasuwa ita ce matsalar.
“Kalubale ga kasar Nijar da Najeriya shi ne suna iyaka da su, yau idan aka ce Najeriya ba’a zaman lafiya to Nijar na iya fuskantan kalubale ta hanyar shigowa da kaya, ko lokacin da aka rufe iyaka ka ga misali, to yanzu ma idan aka ce ba’a zaman lafiya akwai zanga-zanga ko baka shiga siyan kaya, idan kana da kaya kana cikin hadari,” in ji Siradjo.
Shima wani dan Najeriya mazauni Birnin N’Konni, mai suna Isah Ibrahim ya ce gaskiya a halin da suke ciki yanzu game da zanga-zanga, sai dai su ce Inna Lillahi Wa’inna Ilahiraji’un, kuma wannan daukan mutane da ake yi a daina.
Ya ce wannan zanga-zangar an yi ta amma ba ta haifa da da mai ido ba, domin abun da suke tunani za ta kawo gyara.
Anasa bangaren wani dan kasuwa da ke zaune a garin Birnin N'Konni a kan iyaka da Najeriya, cewa ya yi, zanga-zangar ta haifar musu da matsaloli da dama.
Yanzu haka dai, ana ci gaba da kira a ciki da wajen Najeriya, ga ‘yan kasar da shugabanninsu da su koyi darasi daga wannan zangar-zangar, domin samun masalaha a kan halin da ta haifar, domin ‘yan Najeriya da makwabtan su, kar su sake fadawa a cikin halin da zanga-zangar ta jefa su.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:
Dandalin Mu Tattauna