Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama gomman masu zanga-zanga a ranar Asabar tare da harba barkonon tsohuwa don wargaza masu zanga zangar da suka yi yunkurin zuwa ofisoshin gwamnati da ke Abuja, babban birnin kasar, a rana ta uku ta zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake yi a kusan fadin kasar.
A jihar Kano da ke arewacin kasar, an harbi akalla mutum daya a wuya kuma an garzaya da shi asibiti, a cewar wani da ya shaida lamarin.
Mutane 13 ne dai aka kashe a ranar Alhamis a lokacin da zanga-zangar ta rikide ta koma tashin hankali, a cewar kungiyar rajin kare hakkokin bil’adama ta Amnesty International, wacce ta zargi ‘yan sanda da yin amfani da harsasai kan masu zanga-zangar.
A ranar Asabar 'yan sanda sun fadi cewa mutane bakwai suka mutu a zanga-zangar cikin kwanaki uku, amma basu dauki alhakin kisan ba. An kama kusan mutane 700 a yayin zanga-zangar, bayan haka jami’an tsaro 9 sun jikkata, a cewar sanarwar ‘yan sandan.
A ranar Asabar masu zanga-zangar sun tattaru a wani babban filin wasa da ke Abuja amma ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen wargazasu a lokacin da suka yi yunkurin yin tattaki akan wata babbar hanya zuwa tsakiyar birnin.
Dandalin Mu Tattauna