Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Masu Zanga-zanga Ba Su Gamsu Da Jawabin Tinubu Ba


Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

‘Yan Najeriya na ci gaba da nuna rashin gamsuwa da jawabin da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Lahadi inda ya rarrashi ‘yan kasar da su kara hakuri kan halin da ake ciki

Tinubu ya yi jawabin ne yayin da ake zanga zangar nuna fushi kan tsadar rayuwa.

Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Masu zanga-zangar tsadar rayuwa wacce aka yi wa taken #EndBadGovernance sun yi dandazo a filin shakatawa na Gani Fawehinmi Freedom Park, Ojota da ke Legas a ranar Litinin, domin ci gaba da zanga zangar duk da jawabin da shugaba Bola Tinubu ya yi a fadin kasar.

Yunkurin ci gaba da wannan zanga-zanga dai ya biyo bayan wata sanarwa da masu shirya boren suka fitar a ranar Lahadi mai dauke da sa hannun Hassan Taiwo, Ayoyinka Oni da kuma Adegboyega Adeniji, a madadin kwamitin tsare-tsare na #EndBadGovernanceInNigeria, inda suka ce jawabin da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi bai amsa bukatunsu ba.

Masu Zanga-zanga
Masu Zanga-zanga

Sun ce sun saurari jawabin da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Lahadin da ta gabata kuma “sun yi la’akari da abin takaici ne kawai” da ya dauki Shugaba Tinubu kwanaki uku kafin yin jawabi ga kasar game da zanga-zangar.

Tinubu ya tabbatar a wani jawabi da aka watsa a fadin kasar a ranar Lahadin da ta gabata cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta saurare da kuma magance matsalolin masu zanga-zangar, yana mai tabbatar da cewa ya ji kiran nasu da babbar murya.

Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja
Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja

"Ina kira ga masu zanga-zangar da masu shirya zanga-zangar da su dakatar da duk wata zanga-zangar da kuma bude hanya don tattaunawa, wanda a ko da yaushe na yarda da shi ok na 'yar karamar dama ne," in ji shugaban.

Amma masu shirya taron dai sun lura cewa wannan ɗaukar shawarar yin jawabi ga al'umma da shugaban ya yi wata "muhimmiyar nasara ce ga ƙungiyarmu."

Ya zuwa yanzu, mun nuna cewa shugaban kasa bai fi sauran kasar karfi ba,” in ji sanarwar.

Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
Matasa masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya

Yayin da suke lura da tayin tattaunawa na shugaba Tinubu, sun lura cewa akwai damuwa a cikin abubuwan da ya fada, kuma shugaban kasar ya ba da umarnin dakatar da zanga-zangar.

“Amma a namu ra’ayin, shugaban kasa ba zai iya mika mana ya kuma sake mayarwa a lokaci guda ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG