Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Ba A Fita Zanga-Zanga A Jihohin Igbo Ba


Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya
Zanga-zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya

A yayin da matasa da dama suka fita yin zanga-zangar lumana a sassa daban-daban na Najeriya don bayyana fushi kan tsadar rayuwa da yunwa da al’ummar kasar suka tsinci kansu a ciki, ba a samu ko motsin haka ba a kudu maso gabashin kasar.

An kuma samu akasin hakan a yankin kudu maso gabashin kasar a rana ta farko jiya Alhamis, kamar yadda wasu a jihohi na yankin suka shaida wa Muryar Amurka.

A cewar Wazirin Hausawa a garin Onitsha na jihar Anambra Alhaji Yusha’u Imam, “An wayi gari yau babu wata matsala, kuma babu zanga-zanga anan garin Onitsha.

"An bude kasuwar Main Market da sauran kasuwanni na jihar Anambra. Sai dai an fuskanci rashin masu zuwa siyayya a kasuwa. Jama’a ba su fito sosai ba, amma kuma komai lami lafiya. Babu wani batun zanga-zanga anan.”

Shi kuwa wani mazaunin garin Aba na jihar Abia Malam Garba Talle ya bayyana cewa, “kowa yana gida kuma jami’an tsaro suna ta zagayawa. An bi umurnin gwamnati ba wanda ya fito zanga-zanga.”

Ko a Enugu da Owerri manyan biranen jihohin Enugu da Imo, jama’a da dama sun kasance a gidajensu, yayin da wasunsu kuma suka fita kamar yadda da dai aka saba yi.

Yanzu tambaya anan ita ce me ye ya sa al’ummar yankin ba su shiga zanga-zangar ba?

“Al’ummar kudu maso gabas ba sa sha’awa. Sun rungumi kaddara bisa halin da ake ciki, kuma suna kara tunani ne kan yadda za su tsira. A yanzu dai ba sa sha’awar wata zanga-zanga,” in ji mazaunin yankin, Injiniya Chris Elumelu.

A cewar Chinwendu Anuka, “mun saba da halin kuncin. Saboda haka ba mu da wani zabi illa mu ci gaba da rayuwarmu da harkokin mu.”

Sai dai Mr. Daniel Okoro ya lura cewa masu zanga-zanga sun yi ne don a tuna wa gwamnati cewa lokaci ya yi da za ta tashi ta dau kwararan matakai wajen kawo karshen halin kunci da ke addabar kasar.

Ya kara da cewa, “Jama’a sun wahala sosai a karkashin wannan gwamnatin a cikin shekara gudan nan, kuma ya kamata ta yi abin da ya dace.”

Bayanai dai sun nuna cewa an bude kasuwanni da shaguna da ofisoshi da dama a fadin yankin kudu maso gabashin Najeriya a yau Juma’a, kuma jama’a sun fito sosai don gudanar da harkokin su na yau da kullum.

Saurari cikakken rahoto daga Alphonsu Okoroigwe:

Dalilin Da Ya Sa Ba A Fita Zanga-Zanga A Jihohin Igbo Ba
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG