Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaftarewar Kasa Da Malalar Tabo Sun Hallaka Akalla Mutane 157 A Habasha


ETHIOPIA
ETHIOPIA

A yau talata hukumomin Habasha suka bayyana cewar, zaftarewa kasa a wasu yankunan kasar masu nisa sakamakon mamakon ruwan sama ta hallaka akalla mutane 157.

Gofa, kudancin Ethiopia, Yuli 22, 2024. (Isayas Churga/Gofa Zone Government Communication Affairs Department via AP)
Gofa, kudancin Ethiopia, Yuli 22, 2024. (Isayas Churga/Gofa Zone Government Communication Affairs Department via AP)

A cewar wani jami’in karamar hukuma, Dagmawi Ayele, kananan yara da mata masu juna biyu na cikin wadanda iftila’in zaftarewar kasar ta rutsa dasu a yankin Kencho shacha gozdi na kudancin Habasha.

ETHIOPIA
ETHIOPIA

A cewar shugaban ofishin sadarwa na shiyar Gofa inda iftila’in ya afku, Kassahun Abayneh, adadin wadanda suka mutu daga mutum 55 din da yake a yammacin jiya litinin zuwa 157 a yau talata kuma an cigaba da aikin lalubo wadanda al’amarin ya rutsa dasu a yankin.

Malalar tabon data afku da safiyar jiya Litinin ce ta birne galibin mutane da al’amarin ya rutsa dasu a yayin da masu aikin ceto ke cigaba da neman masu sauran numfashi a iftila’in zaftarewar kasar data faru a ranar Lahadi a gangaren tsaunuka.

A cewar Ayele, an samu nasarar zakulo akalla mutane 5 da ransu daga karkashin tabon.

Ethiopia Map
Ethiopia Map

Shima wani jami’i a yankin Gofa, Markos Melese, yace har yanzu ba’a san inda mutane da dama suka shiga ba daga cikin ayarin wadanda tabo ya birne yayin da suke kokarin ceto wasu.

Melese wanda ya kasance darakta a ma’aikatar yaki da bala’o’i ta yankin Gofa yace, har yanzu muna neman wadanda suka bata.

Zaftarewar kasa ta zama ruwan dare a lokacin daminar kasar Habasha, wacce ke somawa a watan Yuli kuma ake sa ran ta kai har tsakiyar watan Satumba.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG