Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jega A Jana'izar Kwamishinan Zaben Jihar Kano marigari Mika'ilu Abdullahi


Furfesa Attahiru Jega
Furfesa Attahiru Jega

Shugaban Hukmar Zaben Najeriya Furfesa Attahiru Jega ya yaba ma Kwamishinan Zaben Jihar Kano, marigayi Mika'ilu Abdullahi

Shugaban hukumar zaben Najeriya Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya yi magana danagne da rasuwar kwamishinan zabe na jihar Kano, a dai dai lokacin da wasu ‘yan najeriya ke kawo shawarar a sake tsarin kula da lafiyar ma’aikatan zabe a kasar musamman a lokutan zabe saboda kare lafiyar ma’akatan daga rashin tabbas.

Furfesa jega ya yi bayanin ne, bayan jana’izar Kwamishinan Zabe na jihar Kano, marigayi Mikaila Abdullahi, wanda ya rasu da matarsa da ‘yan’yansa biyu, a gidansa da ke Kano sanadiyyar tashin gobara.

Wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya ruwaito Jefa na addu’a ga mamacin da cewa, “Inna lillahi wa inna alaihin raju’un. Ubangiji ya jikan Mika’ilu Abdullahi da rahama da shi da iyalan shi, da mu ka yi rashinsu. Mu na rokon Allah ya ba su Aljanna-Firdausi ya gafarta ma su; kuma wannan babban rashi ne a garemu saboda Malam Mika’ilu mutum ne mai hazaka, kuma mutumin kirki. Kuma ya na cikin wadanda na ke ji da su, saboda irin yadda su ke dauka aiki – su na yi fisibilillahi – ana samun nasara.”

Daya daga cikin ma’aikatan gidan mai suna Malam Habibu Yusuf ya ce da shi da wasu ‘yan sanda masu gadi a gidan, suna zaune wajen misalin karfe hudu, sai daya dan sandan ya je tarfo ruwa a famfo, sai kawai ya ga wuta sai shi Malam Habibu ya je ya kashe janareto. Su ka yi ta kokarin kashe wutar har sai da daya dan sandan ya yi ta faduwa har sau hudu sun a janye shi. Sun yi iya yinsu, amma ba a yi sa’a ba. Ya ce mamacin dattijon arziki ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG