Dan Majalisar Jihar mai wakiltar Kurfi kuma zabebben dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Dutsen-Ma da Kurfi, Alhaji Danlami Muhammad Kurfi ya koka kana bin da ya kira yinkurin gwamnan jihar Katsina na sayan kuri’u ta wajen yaudarar mutane da samar da ayyukan yi mara dorewa kuma a kurarren lokaci. Ya ce ko S.A. da aka dauka guda 90 a kowace karamar hukuma ba su samun albashi akan kari.
Ya ce don haka kiran da gwamna Shema ya yi cewa Shugabannin Kananan Hukumomi su dau ma’aikata 500, yaudara ce kawai tunda a baya ya ki daukar ma’aikata saidai wadanda su ka mutu da aka samar da masu maye gurabansu. Ya ce ikirarin samar da ayyukan yi din duk dabara ce ta a zabi PDP. Da wakilinmu Muhammad Rabi’u ya tambaye shi ko baya ganin za a dauka cewa su ‘yan APC sun firgita ne su ke wannan korafin, sai ya ce sam ba haka ba ne. Ya ce duk wanda aka bas hi wani abu wai don ya zabi PDP ya karba, amma ranar zabe ya je ya zabi wanda ya dace.
Da wakilinmu Muhammad Salisu Rabi’u ya tambaye shi ko bai ganin cewa yawancin wadanda su ka yi nasara a APC sun fake ne da farin jinin Buhari, don haka a zabe mai zuwa ‘yan takarar APC za su ji jiki saboda zai zama na kowa tasa ta ficce shi ne, sai y ace ai ba laifi ba ne cin arzikin sunan Buhari, kuma ai su ma ‘yan PDP na da damar cin arzikin sunan gwanayensu.
Y ace duk wani dan PDP da y ace a dawo a yi Buhari mayaudari ne. Y ace idan bah aka ba, me ya sa bai fad aba tuntuni? Y ace amma har yanzu kofar APC na bude don duk mai son tuba, amma bayan kwana 7 za su rufe kofar tuba.
Wakilnmu Rabi’u ya ce jam’iyyar APC ce ta lashe dukkannin kuri’un kujerun ‘yan Majalisar Dattawa da na Wakilai da aka gudanar a jihar katsina.