Wasu ‘yan jam’iyyar PDP daga mazabar Michika da Madagali sun yi barazanar mamaye ofishin INEC saboda wai hukumar ba ta masu adalci ba.
A wani taron manema labarai da wasu jami’an PDP din su ka kira, wanda shi ma wakilinmu Ibrahim Abdul’aiziz ya samu halarta, wani jigon PDP da ya bayyana sunansa da Honorabul Francis Zaman y ace an yi rashin gaskiya a ward din Falam-koji. Ya ce an ba da sanarwar sakamakon zaben Sanata da na Shugaban kasa duk babu na Falam a ciki. Ya ce hukumar ta INEC na nemar haddasa rikici. Y ace sun bai wa hukumar zaben kwanaki biyu su yi abin da ya kamata ko kuma su fuskanci mamaya.
Shi ma tsohon Shugaban Karamar Hukumar Michika Hon Ayuba Tari y ace sun a ma iya zuwa ofishin na INEC su hana su barci.
To saidai wakilinmu Ibrahim ya ce hukumar ta INEC ta fidda wata sanarwa, inda ta ke bayyana cewa ta soke sakamakon Falam da Pujiti ne da ke mazabar Michika a jihar ta Adamawa saboda a sake. To saidai a cewa Ibrahim, a jihar Taraba ‘yan APC ne ke zargin an masu cogen kuri’u a zabukan ‘yan Majalisun Dattawa da Wakilai, musamman ma a mazabun Taraba ta tsakiya da sauran wurare.