Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Darajar Naira Bayan Zaben Shugaban Kasa


Jonathan Da Buhari
Jonathan Da Buhari

Daya daga cikin abinda ke tadawa ‘yan Najeriya hankali shine yadda darajar Naira ke ta faduwa a kullum safe.

"Kafin zabe muna sayenta har 224 zuwa 225 ma. Yanzu kuwa maganar da nake ma a bayan zaben nan in ma ka zo da dalar ba za a sayeta ya wuce Naira 190 ba”.

Alhaji Labaran sakataren Kungiyar ‘yan canjin kudi a Abuja ne wanda ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina haka a hirar da ya yi da shi.

Tsohon shugaban bankin Ja’iz a Najeriya kuma masanin tattalin arziki Mohammed Mustapha Bintube ya bayyana dalilin da ya zama daya daga cikin wadanda suka kada darajar nerar. Yace, “cinikin man fetur na dalar Amurka biliyan 99 a shekarar 2011.

Amma yanzu a shekarar 2014 data gabata kudin da muka samu sun koma dala biliyan 77. Hakan yana da alaka da maganar siyasa.” Kamar yadda Bintube ya bayyana.

Ya kara da cewa maganar barazanar cewa ‘yan kudu zasu yi bore in basu ci zabe bay a taimaka wajen kawo nakasu inda masu zuba jari suka dinka kwashe nasu ya nasu suna barin Najeriyar.

Abin jira anan shine, yadda makomar darajar Naira idan zababben shugaban kasar Muhammadu Buharti ya karbi ragamar mulki daga hannun shugaba Jonathan Goodluck zata kasance.

Darajar Nairar Najeriya Bayan Zaben Shugaban Kasa - 2'59"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG