Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Karyata 'Yan Takarar Gwamna Karkashin PDP Da Ke Cewa Ya Amince A Zabe Su


Shugaban Najeriya Mai Jiran Gado Janar Muhammadu Buhari (murabus)
Shugaban Najeriya Mai Jiran Gado Janar Muhammadu Buhari (murabus)

Janar Buhari ya ce a zabi APC sak a zabukan da ke tafe. Ya karyata 'yan PDP masu cewa ya amince a zabe shi.

Shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari (murabus) ya karyata rade-radin da ake bazawa cewa ya na goyon bayan wasu ‘yan takarar gwamna karkashin jam’iyyar PDP.

Wannan bayanin na Buhari na zuwa ne a daidai lokacin da shi kuma ciyaman din jam’iyyar PDP na kasa tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Ahmed Mu’azu ke hasashen nasarar jam’iyyarsu ta PDP.

Wakilinmu a Babban Birnin Tarayyar Najeriya Abuja, Nasiru Adamu Elhekaya ya ce Janar Buhari ya yi wannan bayanin ne yayin da ya saurari jawabi daga Sanata Danjuma Goje game da gagarumar nasarar da jam’iyyar APC ta samu a sabuwar Majalisar dattawa ta takwas, inda ya ce, “Mu na fata mutanen Gombe za su fito kwansu da kwarkwatansu su zabi APC – da gwamna da ‘yan Majalisarsu ta jiha – abin da mu ke fadi kenan duk inda mu ka je. Wadanda su ka je su ka ba da wani labari na dabam, wannan labarinsu ne, amma ni abin da mu ke fadi Kenan.

Janar Buhari ya ce duk wanda ke so a zabe shi karkashin APC to ya shiga APC ya bi ka’idar zabe a APC. Shi ma Sanata Danjuma Goje ya bukaci da a zabi ‘yan takarar APC a zabukan da ke tafe.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG