Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

2023: NNPP Ta Tsayar Da Kwankwaso A Matsayin Dan Takararta


Dr. Rabiu Musa Kwankwaso (Hoto: Facebook/Rabiu Musa Kwankwaso)
Dr. Rabiu Musa Kwankwaso (Hoto: Facebook/Rabiu Musa Kwankwaso)

Hakan na nufin Kwankwaso, wanda da mamba ne a jam’iyyar PDP da APC, zai yi takara da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar ta PDP. Kazalika zai kara da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu wanda jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar.

Sabuwar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party ta NNPP, ta zabi tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa da za a yi badi.

Jam’iyyar ta zabi Kwankwaso ne a babban taronta da ta yi a Abuja a ranar Laraba. Kwankwaso ya tsaya takarar ne shi kadai ba tare da hamayya ba.

Tun a karshen makon da ya gabata, shugaban jam’iyyar na farko Dr. Boniface Aniebonnan ya bayyana cewa za su yi wannan gangami ne kawai don su tabbatarwa da Kwankwaso takararsa.

Daliget daga kananan hukumomin Najeriya 744 ne suka hallara a filin wasa na Mashood Abiola da ke babban birnin Najeriyar inda suka tsayar da tsohon ministan tsaron a matsayin dan takararsu.

Hakan na nufin Kwankwaso, wanda da mamba ne a jam’iyyar PDP da APC, zai yi takara da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam’iyyar ta PDP.

Kazalika zai kara da tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu wanda jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar.

Tabbatarwa da Kwankwaso takararsa na zuwa ne sa’o’i bayan da jam’iyyar ta APC ta sanar da nasarar Tinubu wanda ya samu kuri’a 1,271 a zaben fitar da gwani a jam’iyyar.

A ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 za a gudanar da zaben shugaban kasar a Najeriya yayin da Shugaba Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa a ranar 29 ga watan Mayu.

XS
SM
MD
LG