Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Ce Lokaci Ya Yi Da Zai Yi Mulkin Najeriya A Zabe Mai Zuwa


Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu

Fitaccen dan siyasar Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya ce lokaci ya yi da zai jagoranci kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, bayan da goyon bayansa ya taimaka wajen tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari kan karagar mulki shekaru bakwai da suka gabata.

Najeriya za ta kada kuri'a domin zaben sabon shugaban kasa a watan Fabrairu mai zuwa. Jam’iyyar APC mai mulki ta Buhari za ta zabi dan takararta na shugaban kasa a babban taron kwanaki uku da za a fara ranar Litinin.

Buhari bai bayyana wanda zai gaje shi ba tukuna yayin da zai sauka daga mulki bayan shekaru takwas da kundin tsarin mulki ya ba shi dama, amma ya bukaci gwamnonin APC su mara ma zabin sa baya.

Tinubu wanda jigo ne a siyasance daga Legas, ya hade jam’iyyarsa da ta Buhari a shekarar 2013 inda suka kafa jam’iyyar APC, wanda a karshe ya baiwa Buhari nasara, wanda ya sha kaye a zabukan shugaban kasa uku da suka gabata.

A wani jawabi da ya yi a gidan talabijin na cikin gida ranar Juma’a, Tinubu mai shekaru 70 a duniya ya shaida wa taron jam’iyyar a jihar Ogun cewa ya goyi bayan Buhari kan fahimtar cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Yanzu lokaci na ne, ina da ilimi, ni kwararre ne, na kuma dade ina yi maka hidima (Buhari), ka bani shugabancin, lokaci na ne,” in ji Tinubu.

"Ba don na mara ma Buhari baya ba, da bai zama shugaban kasa ba."

Har yanzu dai ba a samu mai magana da yawun shugaban kasar ya mai da martani ba.

Ana kallon Tinubu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin ‘yan takara da ke kan gaba a zaben fidda gwani na shugaban kasa, wanda ‘yan takara 23 ne za su fafata gaba daya.

~ REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG