Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

INEC Ta Yi Hasashen 'Yan Najeriya Miliyan 90 Ne Za Su Kada Kuri'a A Zaben 2023


Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)
Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce tana kyautata zaton a kalla mutanen miliyan 90 za su kada kuri'a a babban zaben kasa mai zuwa na shekara ta 2023.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara ofishin hafsan sojin saman Najeriya IO Amao a Abuja babban birnin kasar.

Shugaban hukumar zaben ya nemi taimakon rundunar sojan saman Najeriya wajen ganin an isar da kayan zaɓe a ƙananan hukumomi a lokaci guda lokacin zabe.

Yakubu yace aiki da rundunar shine mafita wajen kare yiwuwar samun tsaiko wajen isar da kayayyakin zabe musamman a yayin da hukumar ke kokarin ganin tayi zaben gwamna a jihar Ekiti akalla nan da makwanni biyu masu zuwa.

Ya jaddada muhimmancin kai kayayyakin zabe a runfunan zabe 190,000 lokacin zaben 'yan majalisu a duk fadin kasar, wanda ake bukatar ganin anyi zabe a lokaci guda wato daga karfe 8:30 na safe zuwa 2:30 na yamma.

Yayin jawabinsa hafsan sojin saman Nijeriya, Amao yace rundunar a shirye take don ganin ta taimakawa hukumar ta INEC wajen gudanar da ayyukan zabe ba tare da wata matsala ba.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG