Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

APC Ta Zabi Tinubu A Matsayin Dan Takararta A Zaben 2023


Lokacin da shugaba Buhari ya ba Tinubu (tsakiya) tutar jam'iyya (Hoto: Fadar shugaban kasa).
Lokacin da shugaba Buhari ya ba Tinubu (tsakiya) tutar jam'iyya (Hoto: Fadar shugaban kasa).

An yi ta kai ruwa rana kafin APC ta kai ga gudanar da wannan babban taro, inda aka yi ta samun baraka a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar kan wanda za a tsayar.

Tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben fitar da gwani a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben da jam'iyyar ta yi don tsayar da wanda zai wakilce ta a zaben shugaban kasa a badi.

Shugaban kwamitin zaben, Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ne ya sanar da sakamakon zaben bayan da aka kamalla kidaya kuri'un.

Tinubu, wanda jigo ne a jam’iyyar ta APC ya samu kuri’a 1,271 a zaben wanda aka fara a ranar Talata zuwa yinin Laraba a filin Eagle Square da ke Abuja, babban tarayyar Najeriya.

Tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi, ya samu kuri’a 316, sai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbaji da ya samu kuri’a 235.

Tinubu yana gaisawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda shi ma ya tsaya takarar neman tikitin jam'iyyar
Tinubu yana gaisawa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda shi ma ya tsaya takarar neman tikitin jam'iyyar

Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya samu kuri’a 152.

A daren ranar Talata da taron ya kankama, wasu daga cikin ‘yan takarar sun janye takararsu tare da nuna goyon baya ga Tinubu a lokacin da suke jawabin neman goyon baya.

Tsohon gwamnan Akwa Ibom Godswill Akpabio ne ya fara nuna goyon bayansa ga Tinubu.

Daga baya sai tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun da tsohon gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi su ma suka mika wuya tare da nuna goyon baya ga Tinubu.

Sauran ‘yan takarar da suka nuna goyon baya ga Tinubu sun hada da tsohon kakakin majalisar wakilai Dimeji Bankole, gwamnan jihar Jigawa Muhammadu Badaru da sauransu.

Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Bola Tinubu)
Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Bola Tinubu)

Wannan sakamako na nufin Tinubu zai kara da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar wanda babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar a matsayin dan takararta a zabe na 2023.

An yi ta kai ruwa rana kafin APC ta kai ga gudanar da wannan babban taro, inda aka yi ta samun baraka a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar kan wanda za a tsayar.

Lamarin ya kai ga shugaban jam’iyyar ta APC Sanata Abdullahi Adamu ya sanar da cewa an cin ma matsayar tsayar da shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan, amma fadar shugaban kasar ta nesanta kanta da zabin.

Mai dakin Tinubu, Remi tana gaishe da shugaba Buhari
Mai dakin Tinubu, Remi tana gaishe da shugaba Buhari

Su ma gwamnonin jam’iyyar da kwamitin gudanawa sun nuna rashin amincewar su da zabin na Adamu.

Shugaba Buhari wanda ke wa’adinsa na karshe, ya ki amincewa da nuna zabinsa a cikin ‘yan takara 23 da suka nuna sha’awar maye gurbinsa idan ya kammala wa’adin mulkinsa, lamarin da wasu suka ce shi ya haifar da rudani a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

Sai dai shugaban na Najeriya ya ce ba ya so ya yi katsalandan wajen zaben magajinsa inda ya mika ragamar zabin ga gwamnonin jam’iyyar da su fitar da wanda suka ga ya fi dacewa.

Tun gabanin haka, gwamnonin jam’iyyar ta APC da suka fito daga arewacin kasar, sun mika tikitin takarar ga kudanci, a wani abu da suka kira tabbatar da adalci a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar wacce ta kwashe shekara bakwai tana mulki ya zuwa yanzu.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaba Bello ya nuna adawarsa da matsayar mika mulkin ga kudu ko tsayar da wani dan takara a matsayin na sasanci.

Saurari cikakke rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:

APC Ta Zabi Tinubu A Matsayin Dan Takararta A Zaben 2023 - 2'07"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG