Dokar an kakabawa jihar ne biyo bayan harin da 'yan Boko Haram suka gudanar a makonni hudu da suka shige.
Jam'iyyar tayi wannan zagi ne a taron manema labarai da ta kira a garin Gombe fadar gwamnatin jihar Gombe. Onarebul Sani Dugge darakta janar na yakin neman zabe a jam'iyyar yace an sa masu dokar takunkumin yawon dare daga karfe shida na safe zuwa goma na dare. Watau karfe goma na dare kowa zai shiga gidansa sai kuma shida na safe. A lokacin zabe ba'a son takaita zirga-zirgan jama'a. Yayi zargin PDP na anfani da dokar ne domin su tozarta masu domin kada su zabi abun da suke so.
Sanata Sa'idu Umar Kumo daraktan yakin neman zabe a jam'yyar PDP ya mayarda martani akan zargin da APC tayi. Yace zargin na APC bashi da tushe. Yace dokar hana fita daga karfe goma na dare har zuwa shida na safe doka ce ta kare lafiyar jama'a da dukiyoyinsu. Yace ba dadi ne ya kawo dokar ba. Kuma duk lokacin da gwamnati da jam'an tsaro suka ga babu wata barazana ga zaman lafiya zasu dageta.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.