Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Shugabannin Kiristoci da Musulmai Sun Kira Matasa Su Gujewa Rikici


Shugabannin addinai
Shugabannin addinai

Yayinda za'a fara zabe gobe shugabannin addinin Kiristanci da Musulunci sun kira matasa su gujewa rikici lokacin zabe da ma bayan zaben

Shgabannin addinan biyu suna kiran mutanen Najeriya musamman matasa da kada su yadda a yi anfani dasu wurin tada zaune tsaye lokacin zabe da ma bayan an kammala zabukan.

Limamin mijami'ar Bishara Baptist ta Sabon Ibadan Philip Mayango ya kira 'yan Najeriya musamman matasan kiristoci su fahimci nufin Allah. Wannan ko shi ne yin zabe cikin zaman lafiya ba tare da tada hankali ba. Su roki Allah ya bada wanda zai rike al'ummar kasar ba sai sun nemi wannan da tashin hankali ba. Allah yana son a kaunaci juna. Sabili da haka kowa ya dauki katin zabensa ya je ya jefa kuri'a domin Allah zai nunawa mutum wanda yake so ya ba shugabanci. Yace a yi gaskiya domin ita ce zata bada abun da ake so.

Malam Dahiru Abubakar mazaunin Sabon Ibadan limamin anguwar 'yan shadda ya kira musulmai matasa su fito cikin kwanciyar hankali ranar zabe su zabi wanda suke so ba tare da rigima ba. Kada su yadda da 'yan siyasar da zasu basu kudi su tada zaune tsaye. Idan wani abu ya faru matasan ne zasu yi asara kila ta rayuka da dukiyoyinsu. Su yi zabe lafiya su koma gidajensu lafiya. Yace addinin musulunci addini ne dake son zaman lafiya. Bai yadda a cutar da kowa ba. Ya kira matasan musulmi su yi zabe cikin kwanciyar hankali da tsanaki.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG