Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Jam'iyyun APC da PDP: Kowacce Tayi Ikirarin Lashe Zabe


Buhari da Jonathan.
Buhari da Jonathan.

Manyan jam'iyyu biyu dake kan gaba sun yi ikirarin lashe zaben da za'a yi ranar Asabar.

Mai magana da yawun PDP Oliseh Metuh yace sun kama hanyar lashe zaben da za'a yi.

Inji Oliseh Metuh jam'iyyarsu ta PDP tana da goyon baya a duk jihohi da shiyoyin kasar shida. Yace banda lashe jihohin da dama na PDP ne irin su Sokoto, Kano, Nasarawa, Rivers, Imo da Kwara zasu lashe jihohin da jam'iyyar adawa ke da tagomashi.

Yawancin jihohin da Olise Metuh ya ambato jihohin gwamnonin nan ne da suka yi adabo da jam'iyyar PDP suka koma ta adawa.

Amma shugaban ma'aikatan Janar Buhari Kanar Hamid Ali yace a'a. Su 'yan APC ke da goyon bayan jama'ar Najeriya. Yace jam'iyyar da kuma dan takararta Janar Buhari suna kara farin jini da samun karbuwa wajen jama'a sabili ke nan da jam'iyyu 13 suka fito suna marawa Janar Buhari baya. Wannan irin tagomashin zai kai jam'iyyar ga lashe zabe.

Tsohon gwamnan Sokoto Attahiru Bafarawa yau shi ne yake yiwa Jonathan kemfen yayin da tsohuwar jam'iyyarsa ta dukufa wajen neman an zabi Janar Buhari. Abubakar Atiku Yusuf sakataren labarun jam'iyyar yace sun dauki Janar Buhari a matsayin dan takarar jam'iyyarsu ta DPP sabili da cancantarsa. Yace kasar tana bukatar ceto kuma Buhari ne zai iya ceto kasar.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG